1 Corinthians 14

1Ku dafkaci kauna kuma ku himmatu domin baye bayen ruhaniya, musamman domin kuyi anabci. 2Domin wanda yake magana da harshe bada mutane yake magana ba amma da Allah. domin babu mai fahimtarsa saboda yana zancen boyayyun abubuwa ciki Ruhu. 3Amma wanda yake anabci da mutane yake magana domin ya gina su, ya karfafa su, kuma ya ta’azantar dasu. 4Wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ginawa, amma mai yin annabci kuwa, ikilisiya yake ginawa.

5To, fatana ace dukan ku kuna magana da harsuna. Amma fiye da hakama, fatana ace kuyi anabci. Wanda yake anabci yafi wanda yake magana da harsuna ( sai dai idan wani ya fassara domin ikilisiya ta ginu). 6Amma yanzu, ‘yan’uwa, in na zo wurin ku ina magana da harsuna, ta yaya zaku karu dani? ba zaya yiwu ba, sai idan nayi maku magana da wahayi, ko sani, ko anabci, ko koyarwa.

7Idan kayan kida marasa rai suna fitar da sauti - kamar su sarewa da algaita - kuma basu fitar da amo daban daban, ta yaya wani zaya san irin amon da sarewar da algaitar suke kadawa? 8Domin idan aka busa kaho da sauti marar ma’ana, ta yaya wani zaya san lokacin da ya dace ya shirya zuwa yaki? 9Haka yake game da ku. Idan kuka furta zance marar ma’ana, ta yaya wani zaya fahimci abinda kukace? zaku yita magana, kuma babu wanda zaya fahimce ku.

10Babu shakka akwai harsuna daban daban a duniya, kuma babu wanda baya da ma’ana. 11Amma idan ban san ma’anar wani harshe ba, zan zama bare ga mai maganar, kuma mai maganar zaya zama bare a gareni.

12haka yake gare ku. Tun da kuna da dokin bayyanuwar Ruhu, ku himmatu da habaka cikin gina ikilisiya. 13To wanda yake magana da harshe yayi addu’a domin ya iya fassarawa. 14Domin idan nayi addu’a da harshe, ruhuna yayi addu’a, amma fahimtata bata karu ba.

15To, me zan yi? Zan yi addu’a da ruhuna, in kuma yi addu’a da fahimtata. Zan yi raira waka da ruhuna, kuma in raira waka da fahimtata. 16In ba haka ba, idan ka yi yabon Allah da ruhu kawai, ta yaya wanda yake waje zai ce, “Amin” a kan godiyar da kake yi in bai san abin da kake fada ba?

17Babu shakka kayi godiya sosai, amma wanin baya ginu ba. 18Nagodewa Allah ina magana da harsuna fiye da ku duka. 19Duk da haka dai a taron ikilisiya na gwammace in yi magana da kalmomi biyar cikin fahimta saboda inganta wadansu fiye da dubu goma da harshe.

20‘Yan’uwa, kada ku zama yara cikin tunani, sai dai a wajen aikin mugunta, ku yi halin jarirai, amma a tunaninku ku girma. 21A rubuce yake a shari’a cewa, “zan yi magana da mutanen nan ta wurin mutane masu bakin harsuna, da kuma lebunan baki. Duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba”, in ji Ubangiji.

22Amma harsuna alamu ne, ba ga masu bada gaskiya ba, sai dai ga marasa ba da gaskiya. Annabci kuwa alama ce ga masu ba da gaskiya, amma ba don marasa bangaskiya ba. 23Saboda haka, in dukan ikilisiya ta taru, kowa kuwa yana magana da wasu harsuna, wadansu na waje da kuma marasa ba da gaskiya suka shigo, ashe, ba sai su ce kun haukace ba ba?

24In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko wani daga waje ya shigo, maganar kuwa zata ratsa shi. Za a ma hukanta shi a kan maganar, 25asiran zuciyarsa kuma za su tonu. Sakamokon haka, sai ya fadi ya yi wa Allah sujada, zaya furta cewa lallai Allah yana tare da ku.

26Sai me kuma ‘yan’uwa? idan kuka tattaru, wani yana da zabura, koyarwa, wahayi, harshe, ko fassara. Kuyi komai domin gina ikilisiya. 27Idan wani yayi magana da harshe, bari a sami mutum biyu ko uku a yawansu, kuma kowa yayi daya bayan daya. Sai wani ya fassara abinda aka fada. 28Amma idan babu wanda zaya fassara, bari dukansu suyi shiru a ikilisiya. Bari kowa yayi wa kansa maganar a gida shi kadai da kuma Allah.

29Bari annabawa biyu ko uku suyi magana, bari sauran su saurara tare da bambance abinda ake fada. 30Idan kuma anba wani fahimta wanda yana zaune a cikin sujadar, bari wanda yake ta magana kafin yanzu yayi shiru.

31Dukanku kuna iya yin annabci daya bayan daya, domin kowannen ku yayi koyi, a kuma samu karfafawa. 32Gama ruhohin annabawa suna karkashin annabawa, 33domin Allah ba Allahn rudu ba ne, na salama ne. Haka yake kuwa a duk ikllisiyoyin masu bangaskiya.

34Mataye suyi shiru a ikilisiyoyi. Domin ba a basu dama ba suyi magana. A maimako, su zama masu sadaukar da kansu, kamar yadda doka ta ce. 35Idan akwai abinda suke so su koya, bari su tambayi mazajen su a gida. Domin abin kunya ne mace tayi magana a ikilisiya. 36Daga wurinku maganar Allah ta zo ne? ko kuwa a gare ku kadai ta iso?

37In wani yana zaton shi ma annabi ne, ko kuwa mai ruhaniya, to, sai ya fahimta, abin nan da nake rubuta maku umarni ne daga wurin Ubangiji. 38In kuwa wani ya ki kula da wannan, shi ma kada a kula da shi.

39Saboda haka, ‘yan’uwa, ku yi marmarin yin annabci sosai, sa’an nan kada ku hana kow yin magana da harsuna. Sai dai a yi komai ta hanyar da ta dace bisa ga tsari.

40

Copyright information for HauULB